1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ongwen zai yi zaman kaso na shekaru 25

Ahmed Salisu
May 6, 2021

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC ta yanke hukuncin shekaru 25 kan wani kwamanda na kungiyar 'yan tawayen nan ta LRA saboda samunsa da aikata laifukan yaki.

https://p.dw.com/p/3t3R3
Niederlande Dominic Ongwen
Hoto: picture alliance picture alliance/dpa/M. Kooren dpa/P. Dejong

A cikin watan Fabrairun da ya gabata ne dai kotun ta sami Dominic Ongwen dan shekaru 45 da haihuwa, da laifukan yakin da yawansu kai 61 ciki har da kisan kai da laifukan da ke da nasaba cin zarafi ta hanyar lalata a lokacin da Joseph Kony ke jagorantar kungiyar ta LRA.

Gabannin yanke hukuncin, masu gabatar da kara sun bukaci da yanke wa Ongwen da aka fi sani da suna ''White Ant'' shekaru 20, sai dai kotun da ke zamanta a birnin Hague na kasar Netherlands ta zabi kara shekaru 5 kan abin da masu gabatar da kara suka nema.