Odinga ya rantsar da kansa shugaban Kenya | Siyasa | DW | 30.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Odinga ya rantsar da kansa shugaban Kenya

Madugun adawa a kasar Kenya Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban al'umma, to sai dai lamarin ya sanya jama'a cikin fargaba.

Bayan yin mubaya'a ga dukkanin bangarori Odinga yace ya sha rantsuwar kama aiki a mastsayin shugaban al'ummar kasar Kenya. yana mai alkawarin yin gaskliya da adalci ga daukacin al'ummar Kenya. Yace zai kiyaye da kuma kare dokokin kasar Kenya tare da martaba da 'yanci da kuma mutuncin kowa da kowa a Kenya. 

Gwamnatin kasar kenya dai ta yi gargadin haramcin kan gangamin rantsuwar a kafofin watsa labaran kasar, da katse shirye-shiryen wasu manyan gidajen talabijin da radio. Malvin Otieno na cikin dubban magoya bayan Odinga da suka yi Allah wadai da matakin gwamnati na sa wa tashoshin talabijin takunkimi.

Kenia Ausschreitungen Opposition Anhänger Odinga (picture-alliance/AP/B. Inganga)

Jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana

"Na samu labarin rufe wasu gidajen watsa labarai da safe, bamu ji dadin haka ba. Ina kallon gangamin a gida amma matakin kastewar ya tilastani zuwa harabar taron don na sheda wa idanuna. Wannan shi ya sa na zo."

Wasu rahotannin bidiyo sun nuna wasu 'yan sanda na arangama da magoya bayan Odinga da ke lalata kadarorin gwamnati. Amma Madugun 'yan adawan da ya sha rantsuwar kama aiki, ya yiwa gwamnati raddi kan matakin da hukumomin ke dauka kan magoya bayansa.

Kenia Nairobi Großdemonstration der Opposition (Reuters/B. Ratner)

Cincirindon magoya bayan Odinga a Nairobi

"A yau rana ce da ta shiga tarihi ga al'ummar kasar kenya, a karon farko dubban mutane sun yi cicirindo a wannan fili. Ina matukar godiya da irin jajircewa da hakuri da al'ummar Kenya suka nunawa sauran duniya cewa mutanen da suke da hadin kai ba'a taba cin galaba a kansu."

Duk dai da cewa kawo yanzu Raila Odinga ya rantsar da kansa ne a matsayin shugaban al'umma ba shugaban kasa ba, amma wannan kalma mai harshen damo na haddasa fargaba ga makomar siyasar kasar da ke shirin samun shugabnni biyu a karon farko. Amma Lone Felix mai sharhi ne kan al'amuran siyasa a Kenya ya bayyanawa DW yadda yake kallon wannan dabarwa.

"Ina farin ciki da cewa akwai ka'idoji da dokoki wanda shi ne babban fargabar kowa, amma bisa ga abinda ke faruwa yanzu alama ce na rashin daidaito a dimokradiyarmu saboda idan da an bi tsari da ba'a fada cikin halin da ake ciki yanzu ba. Wannan ya nuna cewa akwai matsala a tsarin dimokradiyarmu, wanda kuma ke bukatar mu yi nazari a kai baki daya."

 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin