Odinga ya kira zanga-zanga a ranar zabe | Labarai | DW | 18.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Odinga ya kira zanga-zanga a ranar zabe

Madugun adawa a Kenya Raila Odinga ya yi kira na gudanar da zanga-zanga a ranar da hukumar zaben kasar ta tsayar don sake zaben shugaban kasar da aka soke a baya bisa zargin cewa an tafka magudi.

Raila Odinga a yayin jawabinsa ya ce gangamin na ranar 26 ga wannan watan na Oktoba zai kasance wanda ba a taba gani ba a kasar, a makon da ya gabata dan takarar kujerar shugaban kasar ya sanar da janye takararsa a zaben da aka bukaci maimaitawa bisa wasu manyan kura-kurai, sakamakon zaben na farko ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta nasara.

A daya bangaren kuwa, hukumar zabe a wannan Laraba ta gargadi 'yan takara da ma sauran shugabani na jam'iyyun siyasa da su guji tsoma baki cikin lamurran hukumar a yayin da ta ke kokarin ganin ta gudanar da sahihiyar zabe, shugaban hukumar Wafula Chebukati ya yi gargadin ne a yayin ganawa da manema labarai gabanin zaben na mako mai zuwa inda ya nuna yatsa ga jagororin jam'iyyun siyasa a kenya da ya ce sun kasance babban barazana ga demokradiyar kasar.