Obama ya bayyana rashin gamsuwa da siyasar Myanmar | Labarai | DW | 12.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya bayyana rashin gamsuwa da siyasar Myanmar

Take hakkin 'yan jarida da ayyukan bautar da jama'a da aikata fyade da kisan ba gaira ba dalili da mayar da wasu tsirarun kabilu saniyar ware abu ne da ke zama ruwan dare a kasar

Shugaba Barack Obama na kasar Amirka ya bayyana rashin gamsuwar Amurka kan yadda harkokin siyasar kasar Myanmar ke tafiya, inda ya bayyana salon tafiyar mulkin dimokradiyar kasar da cewa ya zo kasa da yadda aka zata.

Shugaba Obaman ya ce akwai tafiyar hawainiya a harkokin siyasar wannan kasa a fannoni da dama, a wasu wuraren ma koma baya ake samu. Ya ce bayan take hakkin 'yan jarida akwai kuma bayyanai kan ci gaban ayyukan take hakkin dan Adam ga ayyukan bautar da jama'a da aikata fyade da kisan ba gaira ba dalili sannan an mayar da wasu tsirarun kabilu saniyar ware.

Wannan bayani na zuwa ne bayan da jagorar 'yan adawa kuma wacce ta ci lambar yabo ta zaman lafiya Aung San Suu Kyi ke cewa abin da shugaba Obama ke tsammanin na ci gaban dimokradiya a kasar ba haka yake ba.

A makon da ya gabata Suu Kyi ta ce babu wani sauyi na ci gaba da ake samu a dimokradiyar kasar ta Myanmar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo