Obama da hakkin dan Adam a Habasha | Siyasa | DW | 27.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama da hakkin dan Adam a Habasha

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bukaci mahukuntan kasar Habasha da su kawo karshen take hakkin 'yan jarida da kuma 'yan adawa a kasar.

Ziyarar Obama a Habasha

Ziyarar Obama a Habasha

Obama ya bukaci hakan ne yayin jawabin da ya yi a taron manema labarai tare da Firaministan Habashan Hailemariam Desalegn bayan da ya isa kasar, a ci gaba da ziyarar aiki da yake a nahiyar Afirka. Kasar Habasha dai ta yi kaurin suna a fage na take hakkin dan Adam ta yadda duk da cewa kasashen duniya na dasawa da ita ta fuskacin hadin kan da take bayarwa wajen yaki da ta'addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a Afirka, suna kuma nuna adawarsu ga yadda mahukuntan kasar ke take hakkin dan Adam musamman ma a bangaren 'yancin fadar albarkacin baki ga 'yan adawar kasar da kuma 'yancin samun bayanai da aiki ga 'yan jarida.

Yabo da gargadi

A jawabin nasa dai Shugaba Barack Obama na Amirka, baya ga yaba wa gwamnatin Habashan da ya yi da kuma bayyana bangarorin da kasashen biyu za su kara karfafa dangantaka tsakanin su da suka hadar da fannin zuba jari da samar da hasken wutar lantarki da tsaro da sauyin yanayi, Obama ya kuma bukaci mahukuntan kasar da su tabbatar da ganin sun kawo gyara a fannin 'yancin dan Adam domin kasar ta samu ci gaba mai ma'ana ya na mai cewa:

Dangantakar shugaban Amirka Barack Obama da Afirka

Dangantakar shugaban Amirka Barack Obama da Afirka

"Samun ci gaba a Habasha ya dogara ne da samun damar yin musayan ra'ayoyi, na yi amanna cewa in har aka ji ta bakin kowa, kuma in har al'umma suka fahimci ana saka su a harkar gudanar da al'amura, hakan zai sa kasar ta samu nasara sosai, mun tattauna matakan da ya kamata gwamnati ta dauka a fannin shugabanci na gari da 'yancin dan Adam da na 'yan jaridu da kuma inganta mulkin dimokaradiyya."

Habasha dai ita ce kasa ta biyu da aka fi daure 'yan jaridu a duniya wanda hakan na daya daga cikin batutuwan da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya ke nuna damuwa a kai, a cewarsu ba a gudanar da cikakken mulikin dimokaradiyya a kasar, ko da yake Firaminista Hailemariam Desalegn na Habashan ya musanta wannan batu ya na mai cewa su na gudanar da mulkin dimokaradiyya yadda ya kamata inda ya ce:

Jawabin kare kai daga zargi

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn

"Gwamnatina na sake jaddada kudirinta na inganta mulkin dimokaradiyya da kuma batun kare hakkin dan Adam da ma shugabanci na gari. Ina kara jaddada cewa a shirye muke mu inganta yanayin dimokaradiyya a kasarmu, mun yi amanna cewa tallafin Amirka a wannan fanni zai taimaka mana wajen samun ci gaba. Mun amince mu ci gaba da karfafa dangantakar da ke takaninmu da Amirka ko da ya ke muna da ban-banci a wasu fannonin musamman ma wajen yanayin yadda muke gudanar da tsare-tsaren dimokaradiyya a kasarmu."

Duk da wannan jawabi da za a iya cewa na kare kai ne da Firaminsta Desalegn ya yi, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch na da ra'ayin cewa batun take hakkin dan Adam a Habasha abu ne da yake a bayyane. A hirar da ta yi da tashar DW mataimakiyar darakta a kungiyar shiyar Afirka Leslie Lefkow cewa ta yi:

"Akwai mutane da dama a tsare a gidan kaso a Habasha wanda bai kamata ace suna tsare ba, akwai 'yan jaridu da masu fafutuka da kuma 'yan adawa, laifinsu kawai shine su na kokarin yin abin da ya ke 'yancinsu ne. A tunanina wannan ba batu ne na rashin shugabanci na gari ba batu ne na gwamnatin Habasha ta kawo karshen cin zarafin dan Adam da ba wai a kasar ne kawai aka hana ko aka yi tir da shi ba har ma a sauran kasashe."

Sauti da bidiyo akan labarin