Nyusi ya sake lashe zabe a Mozambik
October 28, 2019Talla
An sake zaben Shugaba Filipe Nyusi na kasar Mozambik a karo na biyu, inda ya sami kashi 73% na kuri'un da aka kada, kamar dai yadda hukumar zaban kasar ta bayyana a yau Lahadi.
Alkaluman hukumar zaben sun ce abokin takararsa wanda tsohon jagoran kungiyar tawaye na Renamo ne, Ossufo Momade, ya sami kashi 22 na kuri'un.
An dai sa ran Shugaba Nyusin na jam'iyyar Frilimo ne dai zai yi nasara a zaben, sai dai ba da yawan kuri'un da aka sanar ba.
Zaben da aka yi a ranar 15 ga watan nan na Oktoba, ya kuma samar da 'yan majalisar kasa da kuma wasu wakilai na larduna.