NUT ta nuna alhini ga makomar karatu a jihohin arewa | Siyasa | DW | 22.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

NUT ta nuna alhini ga makomar karatu a jihohin arewa

Kungiyar malaman makarantu a Najeriya, ranar Alhamis ta umurci dukkan malamai su rufe makarantu domin nuna alhininsu na 'yan mata fiye da dari biyu da har yanzu 'yan kungiyar Boko Haram ke rike dasu.

Kungiyar malaman makarantu a tarayyar Najeriya, wato NUT ranar Alhamis ta baiwa dukkan malaman makarantu a karkashin inuwar ta, umarnin da su rufe makarantu domin nuna alhininsu na yara yan mata fiye da dari biyu da har yanzu yan kungiyar boko haram ke rike dasu da kuma tausayawa iyalan malamai 173 da aka kashe suna bakin aiki jihohin Borno da Yobe.

Daya daga cikin malaman makaranta ke kara nuna alhininta da bakin ciki, a madadin iyayen yara yan mata fiye da dari biyu da kungiyar Ahlil sunna liddawa'ati wal jihadi da aka fi sani da kungiyar Boko Haram suke rike dasu yau kwanaki talatin da takwas kuma har yanzu ba'a san inda suke ba. Malam Danjuma Saleh, shine shugaban kungiyar malaman makarantu na jihar Bauchi ya kuma bayyana dalilansu na yin wannan gangami na lumana.

Ita ma wannan malamar kuma uwa, Deborah Bulus, cewa tayi, ko kuma roko da aci gaba da yin addu'oi domin a sako wadannan yara, a kuma ceto illmi daga tabarbarewa. Injiniya Tukur Muhammad, shugaban kungiyar iyaye na kwalejin gwamnatin Tarayya dake Bajoga, yace akwai mafita daga zaman dar-dar da a halin yanzu ake fama dashi a makarantun da suke jihohin arewa maso gabas.

Sauti da bidiyo akan labarin