Nuri Al - Maliki ya kai ziyara farko Amurika | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nuri Al - Maliki ya kai ziyara farko Amurika

Nan gaba ayau ne za a ganawa tsakanin shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, da Praministan Irak Nuri Al-Maliki, a birnin Washington.

A hira da yayi jiya da manema labarai, bayan ganawar sa da Tony Blair a birnin London, Nouri Al-Maliki ya bayana abunda ya kira kyaukyawan sakamakon da ya samu, daga hawan sa karagar mulki, zuwa yanzu, ta fanin maido da zaman lahia a ƙasar Iraki.

To saidai a hannu ɗaya, ya amince da rahoton hukumar kare hakkokin bil Adama ta Majlisar Dinkin Dunia wanda ya ruwaito cewar, kussan mutane dubu 6, su ka rasa rayuka, kuma kussan dubu 7, su ka ji raunuka a ƙasar Iraki, tsakanin watannin Mayu da juni da su ka gabata.

A tantanawar da za a yi, idan an jima, Bush da Al-Maliki za su bitar halin da ake ciki, a kasar ta Iraki, da yaƙe yaƙe tsakanin Isra´ila da Hezbollah, da kuma illolin su ga wanzuwar zaman lahia a Iraƙ.

Nuri Al Maliki na gudanar da wannan ziyara, a daidai lokacin da shugaba Bush, ke fuskantar matsacin karan tsana daga Amurikawa, a game da matsayin Gwamnatin Amurika, a Irak.