Nukiliya: Iran ta gargardi kasashen duniya | Labarai | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nukiliya: Iran ta gargardi kasashen duniya

Iran ta gargadi Amirka da sauran kasashen duniya da su guji matsa mata lamba kan shirinta na nukiliya muddin suna son a cimma matsaya kan shirin nata da cike da takaddama.

Ministan harkokin wajen Iran din Mohammad Javad Zarif ne ya bayyana hakan a matsayin martani ga sakon da shugaban Amirka Barack Obama ya aikewa Iran din cewar duniya za ta cigaba da maida ta saniyar ware muddin ba ta amince an cimma matsaya kan shirin nata na nukiliya ba.

Mr. Zarif ya ce lokaci ya yi da Amirka za ta zabi hanya ta laluma da za ta kai ga cimma matsaya maimakon amfani da matsin lamba kan wannan batu mai cike da sarkakiya. Iran dai na shan suka kan wannan shiri nata da wasu kallo a matsayin na mallakar makamin kare dangi, zargi da ta sha musantawa.