Nkurunziza ya dage zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 11.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nkurunziza ya dage zaben shugaban kasa

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya dage zaben shugaban kasa da ke tafe da mako guda wato daga 15 ga watan Yuli zuwa 21 ga wata.

Gwamnatin Burundi ta dage zaben shugaban kasa da ya kamata ya gudana a ranar 15 ga watan Yuli i zuwa 21 ga wannan wata, sakamakon rikicin siyasa da ake ci gaba da fuskanta dangane da tazarcen shugaban kasa Pierre Nkurunziza. Wannan matakin ya biyo bayan kiraye kirayen da 'yan adawan Burundi da kuma shugabannin kasashen yankin Gabashin Afirka suka yi na dage zaben domin a samu damar warware takaddamar da ake fama da ita. Sai dai kuma masharhanta na ganin cewa dage zaben da mako guda ba zai bayar da damar warware rikicin siyasa da mitsitsiyar kasar ta Tsakiyar Afirka ke fama da shi ba.

Kasashen duniya da dama na ganin cewar yunkurin neman wa'adin mulki na uku na shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ke yi, ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin kasar suka cimma a Arusha na Tanzaniya. Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewar mutane 70 suka mutu a Burundi yayin da sama da dubu 150 suka kaurace wa matsugunansu tun bayan barkewar rikicin tazarcen Nkurunziza a watan Afrilun da ya gabata.