Nkurunziza ya ajiye takararsa a hukumance
May 8, 2015Talla
A kasar Burundi shugaban kasar Piere Nkurunziza ya mika a hukumance takardar neman sake tsayawa takara a karo na ukku a yau wannan duk da boren kwanaki 13 da alummar kasar ke yi na nuna adawa da wannan manufa tasa.
Rahotanni dai sun bayyana cewa da yake jawabi a lokacin da ya iso a cibiyar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar domin gabatar da takarar tasa shugaba Nkurunziza ya sha alwashin murkushe duk wata zanga-zanga da ya ce a halin yanzu ta rikide zuwa bore. Sannan ya kuma sha alwashin wanann zabe zai gudana a cikin konciyar hankali da lumana.
A kalla dai mutane 13 ne suka mutu a yayinda sama da dubu 50 su ka yi gudun hijira a tsawon kwanaki 13 na zanga-zangar nuna kyama ga shirin tazarcen shugaban Nkurunziza.