1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasa Nijar za su sulhunta rikicin zabe

Zulaiha Abubakar
September 27, 2018

Hukumomin Nijar sun aminta da tattaunawa da bangarorin dabam-daban domin warware rikicin siyasar kasar mai nasaba da kundin tsarin zabe, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun Firaministan kasar Malam Brigi Rafini.

https://p.dw.com/p/35YYF
Niger Wahlen 2016
Hoto: DW/B.S. Ahmed

A can baya dai hukumomin sun sha nuna turjiya da cewar ba za su taba dawowa da baya ba game da batun kundin tsarin zaben da majalisar dokokin kasar ta rattaba hannu a kansa tun farkon wannan shekara, Lamarin da ya haifar da ficewar Jam'iyyun siyasa da dama daga bangaren gwamnati tare da shiga adawa. Wannan na a matsayin wani sabon babi a siyasar kasar da ke iya zama silar warware rikicin da ya dauki dogon lokaci yana ruruwa tsakanin 'yan siyasa.

Babban sakataren zartarwa na hukumar tattauna al’amuran siyasar kasar ya tabbatar da cewar ranar daya ga watan Oktoba za a soma zaman tattaunawar, kana tuni bangarorin siyasar Nijar suka fara bayyana matsayinsu na amincewa da zaman sulhun.