1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar dage dokar hana taruwa a wuraren ibada

Gazali Abdou Tasawa
May 13, 2020

Gwamnatin Nijar ta dage dokar rufe wuraren ibada wacce ta dauka a karshen watan Maris a wani mataki na hana yaduwar annobar cutar Corona a kasar.

https://p.dw.com/p/3c9Cn
Niger Moschee in Niamey
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a daren jiya, ta ce ta dauki matakin na bude wuraren ibadar wanda zai fara aiki daga wannan rana ta Laraba a fadin kasar, a bisa shawarar shugabannin addinai na kasar, bayan kuma jin ra'ayin kwamitin kwararru na yakin da cutar ta Covid 19 na kasar dangane da yadda annobar ta fara ja da baya.

Sai dai gwamnatin ta yi kira ga shugabannin addinai da su dauki matakai na kiyayewa da suka hada da feshin magani a wuraren ibadar bayan kowace salla, da tilasta wa kowane mamu saka takunkumi da saka tazara ta akalla mita daya tsakanin mamun da kuma wanke hannuwa da sabuli kafin shiga wuraren ibadar.

Kazalika gwamnatin ta dage daga wannan Laraba dokar hanya yawon dare a birnin Yamai. Sai dai gwamnatin ta yi gargadin yiwuwar sake maido da dokar idan matsalar ta sake yin kamari.