Nijar: Boko Haram ta kashe farar hula 140 | Labarai | DW | 26.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Boko Haram ta kashe farar hula 140

Hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a yankin Diffa na na Jamhuriyar Nijar sun hallaka fararen hula da dama tare da jikkata wasu a yayin da wasu kuma aka yi garkuwa da su don neman kudin fansa.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce akalla mutane 140 ne suka hallaka a tsakanin watanni biyar na farkon wannan shekara a yankin Diffa sakamakon hare-haren mayakan ta'addancin Boko Haram da ke shigowa yankin daga makofciyar kasar tarayyar Najeriya. Rahoton na hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya ce mutanen da suka hallakan daga farkon wannan shekarar zauke yanzu, sun zarta adadin wadanda suka hallaka a shekarar 2018.