1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Adawa ta fice daga gyaran kundin zabe

Mahaman Kanta GAT
November 26, 2018

Kawancen jam'iyyun adawa a Nijar ya janye daga taron gyaran kundin tsarin zabe sabili da yadda bangaren gwamnati ya ki amincewa da gyaran wasu kudurori da za su bai wa adawa damar sa ido a tsarin zaben.

https://p.dw.com/p/38wUS
Hama Amadou
Hama Amadou shugaban Jam'iyyar Lumana Afrika kana madugun 'yan adawar NijarHoto: DW/S. Boukari

Jam'iyyun adawar kasar Nijar sun ce ba batun aya ta takwas na kundin tsarin zabe da aka jima ana cecekuce a kai ba ne dalilinsu na ficewa daga taron gyaran kundin tsarin zaben ba. Ko baya ga wannan batu da ke kawo cikas ga makomar siyasar madugun adawar Hama Amadu wanda kudirin ke iya haramta mashi tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2021, akwai wasu kudurorin da ba su amince da su ba. Daga ciki akwai aya ta 12 ta kundin wacce ta kunshi batun kasafin mambobin kwamitin zartarwa na hukumar zabe ta kasa wato CENI.

Niger Wahlen Kandidat Ibrahim Yacouba
Ibrahima Yacouba shugaban Jam'iyyar MPN kishin kasa ta bangaren adawa a NijarHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

'Yan adawar sun ce daga cikin mambobi takwas da kwamitin zartarwar hukumar zaben ya kunsa a karkashin tanadin ayar ta yanzu, gwamanti za ta samu wakillai shida ita kadai a yayin da adawa za ta samu wakili daya zuwa biyu kawai. Kazalika adawar kasar ta Nijar na bukatar ganin an saka mambobinta a hukumar tsara girgam din zabe na zamani wacce kuma ke da nauyin buga katin zabe, domin a cewar 'yan adawar matsawar babu mutanensu a wannan sashe na aikin zabe to kuwa ana iya satar su a zaben. Akwai kuma batun aya ta 80 da ta 82 ta kundin tsarin zaben wacce ta tanadi tsara shugabannin runfunan zabe da mataimakansu inda a nan ma bangarorin siyasar suka kasa jituwa.