Nigeria na cigaba da binciken cutar masassarar tsuntsye
February 13, 2006Hukumomin lafiya a Nigeria na dakon sakamakon gwajin bincike akan wasu kananan yara biyu wanda ka iya zama karon farko na kamuwa da kwayar cutar murar tsuntsaye nauín H5N1 a tsakanin jinsin bil Adama a Afrika. Yaran wadanda ake zato sun kamu da cutar suna zaune ne a kusa da wata gonar kaji a jihar Kaduna dake arewacin Nigeriar. A kuma jihar Kano hukumomi sun fara wani gagarumin shirin kone kaji a matakin hana yaduwar cutar murar tsuntsayen. A nan Nahiyar Turai, kasar Slovania ta aike da samfurin kwayar cutar masassara tsuntsayen zuwa Britaniya domin gudanar da bincike mai zurfi. A kasashen Italiya da Greece da kuma Bulgaria nan ma, an sami bullar nauin kwayar cutar ta H5N1. A halin da ake ciki kungiyar tarayyar turai ta bukaci jamaá kada su firgita su kuma kwantar da hankalin su. Cutar masassarar tsuntsayen ta hallaka a kalla mutane 90 tun bayan da ta bulla a nahiyar Asia da kuma kasar Turkiya a shekarar 2003.