Niger: Rikicin shugabanci a jam’iyyar Lumana Afirka | BATUTUWA | DW | 25.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jam’iyyar Lumana Afirka ta shiga rudani

Niger: Rikicin shugabanci a jam’iyyar Lumana Afirka

A Jamhuriyar Niger wata dambarwa ta barke a Jam’iyyar Lumana Afirka inda shugaban riko na jam’iyyar Oumarou Noma ya kai karar Hama Amadou a gaban kuliya bisa zargin Hama da sauke shi daga shugabancin jam’iyyar.

Wannan dai shine karon farko da irin wannan rikici ya kunno kai a Jam’iyyar ta Lumana Afirka. Oumarou Noma shugaban riko na jam’iyyar yay i zargin cewa Hama Amadou ba shi da hurumin dakatar da shi bayan da kotu ta yanke wa Haman hukukin dauri a gidan kaso.

Sai dai tuni lauyoyin da ke kare Hama Amadou suka yi watsi da wannan batu. Shi dai Hama wanda yake gudun hijira a kasar waje ya aike da wasika ga Oumarou Noma inda ya sanar da shi cewa ya cire shi daga shugabancin rikon jam’iyyar da ya nada shi batun da Oumarou ya shigar da kara kotun Yamai yana kalubalantar matakin.

To sai dai yayin da lauyan mai shigar da kara ya ce sun shigar da karar ce saboda da Hama Amadou da ke fuskantar hukuncin dauri na shekara daya a gidan yari bashi da wani huuimi na shugabancin jam’iyya ballantana ma ya kori Oumarou Noma daga mukaminsa kuma ko babu komai a cewar mai shigar da karar babban taro jam’iyya ne ya nada Oumarou Noma a matayin shugaban riko na jam‘iyyar Lumana.

A daya sharin kuma lauyoyin da ke kare Hama Amadou a karkashin jagorancin Maitre Mossi sun nuna nasu shaidu cewa kotun ba ta da hurumin na tabo batun haramci ga Hama Amadou hasali ma kuma Hama shine ya aike da wasika ta nada Oumarou Noma mukamin shugabanci jam’iyyar na riko amma ba wai babban taron jam’iyyar ba.

Bayan dukkan bangarorin sun gabatar da hujjojinsu Alkalin kotun ya daga shari’ar inda zai bayar da sakamako ranar Jumma’a 26 ga wannan watan na Yuli.

Sauti da bidiyo akan labarin