Ni ma ɗan Adam ne–‘yan Afirkan da ke fama da taɓin hankali
November 19, 2013Talla
Wannan salsalar ta Ji ka Ƙaru, ta bi rayuwar mutane uku masu fama da taɓin hankali, Amina, Musa da John ya kuma nuna irin ƙalubalen da sukan fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullun. Salsalar ta kuma nuna yadda ‘yanuwa da abokan arziƙin masu fama da wannan naƙassa kan yi ƙoƙarin su fahimcesu su kuma yi aiki tare da su. Masu sauraro zasu koyi cewa mutanen da ke da naƙasar da ta shafi ƙwaƙwalwa, su ma mutane ne kamar kowa kuma sun cancanci a nuna musu ƙauna a kuma mutunta su.
(Saurarin sautin wasan kwaikwayo daga kasa)