1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Shirin kafa gwamnatin hadin gwiwa

Ramatu Garba Baba
April 15, 2020

Nan bada jimawa ake sa ran firaiminista Benjamin Netanyahu zai kafa gwamnatin hadaka da za ta hada da bangaren adawa na Benny Gantz, matakin da ya biyo bayan rashin nasarar da ya yi a zaben kasar.

https://p.dw.com/p/3ax7F
Russland Moskau Benjamin Netanjahu
Hoto: Maxim Shemetov/REUTERS

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na da 'yan sa'oi kafin cikan wa'adin kafa gwamnatin hadaka wanda akasin hakan ka iya jefa kasar cikin sabon rudanin siyasa. Samar da gwamnatin hadin gwiwar zai kawo karshen rikita-rikitan siyasa da kasar ta fada tun Disambar 2018.

Mista Netanyahu ya kasa kafa gwamnati ne bayan rashin nasara na isassun kuri'un da za su ba shi zarafin kafa gwamnati ba tare da hada kai da wasu jam'iyyun siyasa ba. Benny Gantz kuwa na jagorancin wata hadakar jam'iyyu ne masu sassaucin ra'ayi, wannan dai dama ce a gareshi ya hada gwamnatin hadin gwiwar a sakamakon gazawar Firaiminista Netanyahu.