Netanyahu da Benny Gantz ko wane ya yi ikirarin samun nasara | Labarai | DW | 10.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Netanyahu da Benny Gantz ko wane ya yi ikirarin samun nasara

Jam'iyyar firaminista Isra'ila Benjamen Netanyahu na kan hayar samu nasara a zaben yan majalisar dokoki abin da zai ba shi damar yin wa'adi na biyar na mulki.

Rahotannin sun ce bayan kammala kidayar kashi biyu bisa uku na kuri'un, jam'iyyar Likud ta Netanyahu ita ce ke kan gaba a  gaban jam'iyyar masu matsagaicin ra'ayi  da ake kira Fari da Shudi ta  tsohon shugaban soja kasar Benny Gantz. Sai dai a halin da ake ciki a wani taron manema labarai da ya kira abokin adawar na Netanyahu, Benny Gantz shi ma  ya yi ikirarin samun nasara.