Neman magance rikicin Libiya | Labarai | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman magance rikicin Libiya

Majalisar Dinkin Duniya tana tattaunawa domin shawo kan rikicin Libiya

Majalisar Dinkin Duniya tana shirin tattaunawa da tsageru masu dauke da makamai na Libiya da suka karbe iko da wasu sassan kasar, domin janye da zai kare kasar daga fadawa a yakin basasa.

A wannan Litinin da ta gabata, majalisar ta taimaka aka fara tattaunawa tsakanin mambobin majalisar dokokin kasar. Manzon musamman na majlisar a kasar Bernadino Leon ya ce mataki na biyu sasantawar ya yi nisa domin shawo kan tsagerun da ke dauke makaman. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada cikin rudani shekaru uku da suka gabata, sakamakon juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu