1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman kawar da mamayar Isra'ila a Falasdinu

Ahmed SalisuSeptember 26, 2014

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya nemi Isra'ila da ta gaggauta kawo karshen mamayar da ta ke yi wa wasu yankuna na kasar, inda ya ke cewar lokacin samun 'yancinsu ya zo.

https://p.dw.com/p/1DLpr
UN Vollversammlung 26.09.2014 - Mahmud Abbas
Hoto: Reuters/Mike Segar

Abbas ya ambata hakan ne a wani jawabi da ya yi ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya kara da cewar lokaci ya yi da za a baiwa al'ummarsu damar mike kafafunsu kamar na kowacce kasa.

Baya ga wannan ya kuma ce Falasdinu zata nemi hakkinta gaban shari'a game da laifukan yakin da ya ce Isra'ila ta aikata a Gaza lokacin da suka shafe kwanakin hamsin suna tafka fada a kwanakin baya.

Mr. Abbas ya ce ba za su taba yafe abinda aka yi musu ba kuma ba za su mance da kisan al'ummarsu sama da dubu biyu da aka yi ba a yakin wanda galibinsu fararen hula ciki kuwa har da mata da yara kanana.