Neman aiwatar da sauyin siyasa a Sudan | Labarai | DW | 28.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman aiwatar da sauyin siyasa a Sudan

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya yi kira da a gudanar da babban taro domin magance matsalolin da ke ci wa jam'iyyarsa da kuma wasu sassa na kasar tuwo a kwarya.

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya bukaci kusoshin jam'iyyarsa da ke shirin juya masa baya da su zo a zauna kan teburin tattaunawa, domin a gano bakin zaren warware rikicin da ke addabarsu. A lokacin da ya ke jawabin bude sabon zaman majalisa a birnin Khartum, al-Bashir ya ambaci wajibcin gudanar da sauye-sauyen siyasa da kuma gudanar da babban taron kasa domin dora Sudan kan wata sabuwar turba.

Furucin na al-Bashir ya zo ne kwanaki hudu bayan da wani kwamitin bincike da aka kafa a jam'iyyar NCP mai mulki ya shawarci a kori uku daga cikin kusoshin jam'iyyar, bayan da suka soki amfani da karfin da aka yi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a watan Satumban da ya gabata. Sai dai kuma wadannan jami'ai da suka hada da tsohon ministan wasannin Sudan Hassan Osman Rizik sun yi barazanar kafa wata sabuwar jam'iyyar siyasa da za ta kara da ta gwamnati.

Al-Bashir ya kuma jaddada kiran da ya yi a watan Afrilun da ya gabata na gudanar da babban taro wanda zai hada kowa da kowa ciki kuwa harda kungiyoyin tawaye da nufin dinke barakar da kasar ke fama da ita.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh