Nelson Mandela ya cika shekaru 95 da haihuwa | Siyasa | DW | 18.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nelson Mandela ya cika shekaru 95 da haihuwa

Al'umar Afirka ta Kudu sun shirya bukukuwa da fadakarwa domin tunawa da ranar haihuwar dan gaggwarmayar yaki da wariyar launin fata, kana bakar fata na farko da ya shugabanci kasar.

'Yan makarantar sakandare ma sun rere wakoki domin girmama Nelson Mandela. Da ma rukunin makarantarsu na daya daga cikin wadanda shan miyagun kwayoyi ya yi katutu a Afirka ta Kudu, inda za ka samu dalibai da shan miyagun kwayoyi ya yi wa illah sosai. Sai dai kuma wata kungiya mai rajin yaki da shan miyagun kwayoyi mai suna "Verulam Anti-Drug Forum" ta yi amfani da wannan dama domin fadakar da daliban irin fafutukar da Nelson Mandela ya yi domin ya zame musu abin koyi. Jagorar kungiyar Thabo Mokoena, ta bayyana dalilan da suka sanya ta ke amfani da Nelson Mandela wajen yin gangamin yaki da shan miyagun kwayoyin.

Geburtstag von Mandela

'Yan Afirka ta Kudu na alfahari da Mandela

" A duk lokacin da nake gangamin yaki da shna miyagun kwayoyi ina bayyana irin fafutukar da Nelson Mandela ya yi da yadda ya sha wahala kafin ya canza baki dayan duniya ta zamo yadda take a yanzu. Sabo da haka dolene a matsayinmu na matsa mu yi koyi da shi".

Matsayin matasan Afirka ta Kudu a kan Mandela

Wasu matasa sun bayyana cewa suna fatan bin tafarkin Nelson Mandela ta hanyar kauracewa shan miyagun kwayoyi.
"Na ga abubuwa da dama a dangane da Nelson Mandela: da farko ba ya shan miyagun kwayoyi, a matsayinmu na mutane dolen e mu yi tunani ncewa in muna shan miyagun kwayoyi za mu cutar da kanmu."

Su ma dai mata matasa ba a barsu a baya ba wajen bayyan amatsayinsu game da Mandela.
"Shi abun koyi ne, bai taba aikata wani mugun hali ba, kamar a ganshi a jaridu ya na tuki ,ya na shaye-shaye. ya kamata mu yi koyi da shi mu aikata abin da ya yi kafin mu".

18 ga watan Yuli ce ranar Mandela ta duniya

A child reads a message in support of ailing former South African President Nelson Mandela in front of the Medi-Clinic Heart Hospital where he is being treated in Pretoria July 6, 2013. REUTERS/Thomas Mukoya (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS SOCIETY HEALTH)

Ana nuna alhani game da rashin lafiyar Mandela

Majalisar Dinkin Duniya ta ware 18 ga watan Yulin ko wacce shekara domin tunawa da gwagwarmayar da Nelson Mandelan ya yi na gawar da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. To sai dai bikin na 2013 ana gudanar da shi ne a daidai lokacin da Mandelar ke kwance a wani asibiti tun tsahon makwannin shidan da suka gabata. 'Yan Afirka ta Kudu da dama sun ba da mintuna 67 a cikin lokacinsu na wannan rana domin tunawa da shekaru 67 da Mandela ya kwashe ya na gwagwarmayar kwatar 'yanci.

Mawallafi: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin