NDA: Mun fasa bututun mai na NNPC da NPDC | Labarai | DW | 03.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NDA: Mun fasa bututun mai na NNPC da NPDC

'Yan Niger Delta Avengers sun yi ikirarin kai hare-hare biyar da suka lalata bututun mai na kanfofin Chevron da NNPC a kudancin tarayyar Najeriya.

Tsagerun yankin Niger Delta sun dauki alhakin hare-hare biyar da aka kai a kan kadarorin kanfanonin hako mai da iskar gas da ke jihar Delta a Kudancin Najeriya. Cikin wani sako da suka wallafa a shafinsu na Twitter, 'ya'yan kungiyar Niger Delta Avengers NDA a takaice sun yi ikirarin fasa bututun mai na kanfanin NNPC, da wasu karin bututaye biyu na kanfanin NPDC. Sannan suka ce sun lalata rijiyoyin mai na kanfanin Chevron.

Kafofi daban daban ciki har da na tsaro sun tabbatar wa kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP afkuwar wadannan hare-haren, wadanda ke sa harkar hako danyen mai tafiyar hawainiya a Najeriya. Yanzu haka dai ganguna miliyan daya da dubu 600 na mai Najeriya ke fiddawa a rana, sabanin akalla ganganu fiye da miliyan biyu a baya.

Su dai tsagerun kungiyar NDA da suka bayyana a watan Mayun wannan shekarar, sun bayyana burinsu na samar da 'yantaciyyar kasar Biafra, saboda suna ganin cewar yankin Niger Delta ba ya cin gajiya yadda ya kamata na arzikin man fetur da Allah ya hore mata.