Na′urar sanar da gobara | Himma dai Matasa | DW | 18.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Na'urar sanar da gobara

Wani matashi mai suna Taye Fashorun wanda ya kirkiro da wata na'ura mai suna (fire trac) da ke ba da alama da zarar gobara ta kama wacce tuni aka fara mafani da ita a Najeriya.

Matsalolin annobar gobara a mafi yawancin birane da kasuwanni a Najeriya matsalace dake cigaba da ciwa alummar kasar tuwo a kwarya, a don haka hukumomi da kungiyoyi ke ci gaba da fadi tashi wajen ganin an dauki kwararan matakan magance matsalar musamman fadakar da jama'a yin nesa da duk abin da ka iya janyo musabbabin gobarar.

Taye Fashorun wanda da za a iya cewar ya cira tuta domin kuwa shine matashin da a karon farko ya bullo da naurar dake bayar da alamar kamawar gobara gami da kashe ta nan take kana kuma wacce take dauke da lambobin waya sama da dari tare da aike wa da sakonin karta-kwana ga masu dauke da lamboyin waya.

Tuni dai na'urar firetrac aka fara amfani da ita a gidaje gami da ababen hawa a Najeriya.