Nasara a yaki da ta′addancin Pakista | Labarai | DW | 29.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nasara a yaki da ta'addancin Pakista

'Yan sandan kasar Pakistan sun yi nasarar hallaka jagoran kungiyar Sunni wanda ake zargi da kitsa ayyukan ta'addanci a kasar.

Gwamnan Lardin Punjab yace a safiyar yau Laraba 'yan sanda suka yi wa kungiyar kawanya, inda aka hallaka 'yan kungiyar 13 ciki harda shugabansu Malik Ishaq bayan musayar wutab ta sa'o'i biyu. Dama dai tun a makwan jiya ne 'yan sanda suka cafke jagoran 'yan ta'addan, amma gungun wasu magoya bayansa suka kwace shi kafin isa ofishin 'yan sanda. Kungiyar Sunni da Malik Ishaq ke jagoranta ana zarginta da yin sanadiyar mutuwar daruruwan jama'ar Pakistan, musamman 'yan Shi'a marasa rinjaye.