Nasara a kan cutar Ebola a Mali | Labarai | DW | 12.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nasara a kan cutar Ebola a Mali

Ma'aikatar lafiya ta Mali ta sanar da cewa mutum na karshe da ya rage dauke da kwayar cutar Ebola mai saurin kisa a kasar ya samu sauki.

Rahotanni sun nunar da cewa an ma sallami mutumin daga asibiti. A wata sanarwa da ta buga a shafin ta na Internet, ma'aikatar lafiyan ta Mali ta ce an sallami mutumin a Alhamis din nan daga asibitin bayan da aka yi masa gwaje-gwajen cutar ba tare da samun kwayarta a jikinsa ba. Ta kuma kara da cewa a yanzu ba ta da wani rahoto na mai dauke da cutar ko kuma wanda ake zargi ya kamu da Ebolan a kasar, sai dai har kawo yanzu ta na kula da wasu mutane 26 da aka kebe a ke lura da su sakamakon mu'amala da suka yi da masu dauke da Ebolan. Kasar mali dai ta samu masu dauke da cutar har guda takwas duk kansu kuma sun kamu ne sakamakon mu'amala da wasu mutane da suka tsallako daga makwabciyar kasar Guinea inda cutar ta fara bulla. Kawo yanzu dai akallah mutane 6,500 ne aka hakikance cewa cutar ta hallaka a yammacin Afirka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu