1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nan gaba za a fara zaben shugaban Amirka

Abdul-raheem Hassan
November 3, 2020

'Yan Amirka za su tantance wanda zai mulki kasar nan gaba tsakanin Donald Trump na jam'iyyar Republican da ke neman wa'adi na biyu da Joe Biden na jam'iyyar Dimokrat da ke adawa.

https://p.dw.com/p/3kn3t
US Wahl 2020 Endspurt der Kampagne
Hoto: Brandon Bell/Reuters

Akalla 'yan kasar miliyan 100 sun riga sun kada kuri'unsu gabannin ranar ta yau, sai dai batun lokacin sanar da sakamakon zaben ya fara haddasa kumfar baki tsakanin 'yan takarar biyu, yayin da batun ke haifar da shakku ga makomar zaben ga wasu 'yan kasar.

Batun haraji da 'yan gudun hijira da manufofin kasar Amirka a kasashen waje, su ne manyan abinda masu zabe suka fi maida hankali tsakanin 'yan takara biyu da ke zawarcin shiga fadar gwamnatin Amirka ta White House.