Namibiya ta yi sabon shugaban kasa | Labarai | DW | 21.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Namibiya ta yi sabon shugaban kasa

Sabon shugaban kasar Namibiya ya sha alwashin yaki da talauci da rashin dai-daito a tsakanin 'yan kasar.

Sabon shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya yi rantsuwar kamun aiki watanni uku bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar. A yayin da ake rantsar da shi sabon shugaban mai kimanin shekaru 73 a duniya ya sha alwashin yin yaki da talauci da kuma rashin dai-daito a tsakanin al'ummar kasar dake da sama da mutane miliyan biyu. Geingob wanda ke zaman shugaban jami'iyyar South West Africa People's Organisation ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwambar bara da kaso 87 cikin dari tare da zamowa zababben shugaban kasar ta Namibiya na uku tun bayan da ta samu 'yancin kanta daga kasar Afirka ta Kudu a shekara ta 1990.