Najeriya za ta sayo makanan dala biliyan guda | Labarai | DW | 04.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta sayo makanan dala biliyan guda

Najeriya ta bayyana shirin sayen makaman yaki don murkushe ayyukan tarzomar da ke gigita zaman lafiyar Najeriyar. Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya yi wa 'yan kasar maganta matsalar daga tushe.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da yin amfani da dalar Amirka biliyan guda, wajen sayen kayan yaki ga dakarun kasar. Ministan harkokin tsaron Najeriya Mansur Dan Ali, shi ne ya tabbatar da labarin a Abuja babban birnin kasar, bayan kammala wani taro da jagororin hukumomin tsaro da aka yi a wannan Laraba.

Ministan wanda ya ce taron ya mayar da hankali ne kan tsaron cikin kasa, bai dai bayar da cikakkun bayanai kan makaman da za a sayo, ko kuma tushen dala miliyan dubu gudan ba. 

Najeriyar dai na fuskantar tarin matsalolin na tsaro ganin daruruwan rayuka ne ke salwanta a sassa daban-daban na kasar, batun kuma da shugaba Buharin ya yi wa 'yan kasar na maganta masu su.