Najeriya: Taron jihohin Kudu kan harajin VAT | BATUTUWA | DW | 16.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Taron jihohin Kudu kan harajin VAT

Gwamnonin jihohin kudancin Najeriya, sun gudanar da taro a jihar Enugu. Ba wannan ne karo na farko da suka gudanar da irin wannan taron ba, sai dai da alamu wannan karon bai samu tagomashin da ake fata ba.

Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria

Kalubalen hada kan kasa, ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Taron dai ya karkata hankali ne, kan batutuwan da suka shafi harajin VAT da tsaron kan iyakokin jahohinsu da ma batun siyasar 2023. Sai dai kuma ba duka gwamnoni 17 na kudancin Najeriyar ne suka halarci taron ba wasunsu sun tura wakilai ne, inda ma gwamnan jihar Anambra Willie Obiano bai halarta ba bai kuma tura wakili ba.

Karin Bayani:Harajin VAT da tsarin federaliyya a Najeriya

Wannan taro dai da ke zaman na uku tun kirkirarsa da gwamnonin na kudancin Najeriya suka yi, kan batutuwan da suka shafi harajin VAT da wasu jahohin Kudu maso Gabashin Najeriyar kamar Rivers suka fara tsagawa suka jini. Sai batun tsaro da kan iyakokin jahohinsu da hana makiyaya yawon kiwo a yankin, ya sa jihohin na ta kokarin samar da dokoki daga majalisunsu. Wani karin batu da zai dau hankula shi ne na yiwuwar mulki ya koma kudancin kasar kamar yadda kakar zabuka na shekarar 2023 ke karatowa.

Sauti da bidiyo akan labarin