Najeriya ta yi bayani kan kisar ′yan hijira | Labarai | DW | 22.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta yi bayani kan kisar 'yan hijira

Rundunar soji a Najeriya ta fito da wasu bayanai dangane da kisan sakaci da ta yi wa sama da 'yan gudun hijira 100 a kauyen Rann da ke arewa maso gabashin kasar a watannin da suka gabata.

Rundunar mayakan saman kasar ta ce babban dalilin faruwar lamarin, shi ne na rashin shaata sansanin 'yan hijiran cikin taswira ta yadda za su fahimta. Wasu hotunan bidiyo da taurarun dan adam ya nuno, ya bayyana wani taron jama'ar da sojin basu san da su ba, da kuma suka yi zaton mayakan Boko Haram ne da suke kwantonsu a dazukan yankin.

Harin na Bam dai ya halaka galibi mata ne da kananan yara gami da wasu jami'an agaji na Red Cross. Kwamandojin yaki a yankin sun ce hakan, kuskure ne irin na yaki da ba so shi ba.