1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sake asarar dubban biliyoyin Nairori

February 5, 2019

Kasa da makonni biyu da fara zabukan Najeriya, ga dukkan alamu tattalin arzikin kasar ya yi nisa cikin matsalar da ta kai ga asarar kusan Triliyan Uku a kasuwar hannu jari.

https://p.dw.com/p/3Ck2q
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wani sabon rahoto kan tattalin arzikin kasar dai ya ce kasuwar hannun jari ta yi asarar da ta kai tiriliyan uku na Nairar kasar a tsawon wattani Shida kacal.

Tun daga watan Mayun shekarar da ta shude da ke zaman dan ba a siyasar kasar, an kalli raguwa a kasuwar hannun jarin daga tiriliyan 14 cikin watan ya zuwa 11 a karshen watan Janairun da ya shude.

Ka ce na ce a siyasa dai ake ta’allakawa da ummul aba’isin raguwar mai tasiri da kuma ke barazana ga makoma ta tattalin arzikin da ya fito cikin masassara babu dadewa, a fadar malam Yusha’u Aliyu, masani na tattalin arzikin Najeriyar.

Sake komawa a ruwa ko kuma kokari na samar da shugaba dai kama daga ita kanta jam’iyya mai mulkin ya zuwa ragowar da ke adawa dai daga dukkan alamu ba sa kallon makoma ta tattalin arzikin a cikin yakin neman zaben da ke gudana a yanzu.

To sai dai kuma a fadar Buba Galadima da ke zaman kakaki ga adawar, matsalar ta wuce batun kace nace, har ma ta kai ga rashin bin dokokin gwamnatin da ke dada aiken tsura a zukata ta masu takama da kasuwar.

Abin jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa, bayan gama zaben ga kasar da ke da bukatar girma amma kuma ke fuskantar barazana ta rudani.