1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta amince da hukuncin FIFA

August 20, 2018

Najeriya ta amince da shugabancin hukumar kwallon kafa na kasar da hukumar kwallo ta duniya FIFA ta yarda da shi.

https://p.dw.com/p/33Qt7
Nigeria Sportminister Solomon Dalung
Solomon Dalung ministan matasa da wasanni a NajeriyaHoto: DW/U. A. Idris

Najeriya ta amince da shugabancin hukumar kwallon kafa na kasar da hukumar kwallo ta duniya FIFA ta yarda da shi, 'yan mintuna gabanin cikar wa'adin haramta mata shiga manyan gasannin duniya nan gaba.

Dama dai da misalin karfe 12 agogon Najeriyar na wanna Litinin ne wa'adin na FIFA zai cika, kan daukar matakin saboda sa baki da hukumomi suka yi kan zaben jagororin hukumar wasannin kasar da aka yi a baya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriyar ta aike wa FIFA cewar ta amince da jagorancin hukumar ta NFF karkashin Amaju Pinnick.

Da fari dai FIFA ta shirya hana Najeriyar shiga wasannin neman shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ne da za a yi cikin watan gobe.