Najeriya: Kirismeti cikin larurar corona da rashin kudi | Siyasa | DW | 24.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kirismeti cikin larurar corona da rashin kudi

Matsaloli na koma bayan tattalin arziki da kunci rayuwa sun rage armashin yadda mabiya addinin Kirista ke yin bukukuwan Sallah Kirismeti a Najeriya.

A bisa al'ada dai tun ma kafin sallah a kan samun karuwar hada-hadar jama’a a kasuwani da tashoshin mota domin wadanda ke son tafiya don gudanar da bikin tare da ‘yan uwa da abokan arziki. To sai dai a bana abubuwa sun canza  sosai inda babu irin wannan cukunso a mafi yawan tashoshin motar da ke Abuja. Kasuwani da aka saba samu sun tsinke a bana an ga canji na raguwar masu kai da kawo musamman ma dai mata.

Koma bayan tattalin arziki da corona sun yi tasiri wajen rage armashin bukukuwan na Kirismeti a Najeriya

Koma bayan tattalin arziki da Najeriyar ta sake afkawa a ciki dai babban matsala ce ga harkokin yau da kullum a kasar musamman masu karamin karfi da yanayin ya kara jefa su a cikin hali na ‘yan rabana ka wadatamu. Malam Yusha’u Aliyu masani harkokin tattalin arziki a Najeriyar ya bayyana dalilan na tattalin arziki da suka ragewa bikin Kirismetin armashi da cewar babban kalubale ne ga kasar. Pastor Yohana Buru shugaban Cocin Evengelical ne da ke Kaduna: ''Ba da umurnin rufe wuraren shakatawa da klob-klob a Abuja da gwamnati ta yi saboda karuwar cutar Covid 19 da ya fado a wannan lokaci ya ragewa bukukuwan armashi musamman a tsakanin matasa da suka saba ziyaratar wadannan wurare a lokacin hutu.''

Sauti da bidiyo akan labarin