Najeriya: INEC ta magantu kan Zamfara | Labarai | DW | 25.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: INEC ta magantu kan Zamfara

A Najeriya rashin gudanar da zaben fidda gwani a zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki ya yi wa jam'iyyar APC illa a jihar Zamfara, inda hukumar zabe ta ce za ta mika takardun sheda ga 'yan adawa bayan hukuncin kotu.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya INEC Ferfesa Mahmud Yakubu shi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ofishin hukumar da ke a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, inda ya ce bisa jaddada hukuncin babbar kotun kolin Najeriya yanzu haka hukumar INEC ta tantance wadanda suka sami nasara a jihar Zamfara, inda gwamna da mataimakinsa su ne: Bello Muhammed Matawalle da mataimakinsa Mahadi Aliyu Gusau na jam'iyyar PDP. Sanatoci kuwa Zamfara ta Arewa na da Alhaji Ya'u Sahabi yayin da Zamfara ta Tsakiya ke da Muhammed Hassan kana Zamfara ta Yamma Lawalli Hassan Anka ya lashe zaben. Dukkanasu dai 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa ta PDP ne. Hukumar za ta bai wa gwamna da mataimakinsa takardar shaida da sanatoci a ranar Litinin din makon gobe 27 ga watan Mayun da muke ciki, kana su kuma 'yan majalisar dokoki na jiha su karbi tasu takardar shaidar a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Zamfara a ranar 31 ga watan na Mayu.