Najeriya: An sace manoma 22 a kusa da Abuja | Labarai | DW | 24.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An sace manoma 22 a kusa da Abuja

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce wasu ‘yan bindiga sun sace manoma 22 a gonakinsu da ke wajen Abuja babban birnin tarayya a ranar Larabar da ta gabata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Oduniyi Omotayo ya shaida wa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa lamarin ya faru ne a Rafin Daji, da ke tsakanin jihar Neja da kuma yankin babban birnin tarayyar Najeriya. Dama dai masu aikata munanan laifuka sun saba kai hari a yankunan karkara na tsakiya da kuma Arewa maso yammacin Najeriya, amma ba a cika yin garkuwa da jama'a ba a babban birnin tarayya (FCT) da ke tsakiyar kasar ba.

 jami'an ‘yan sanda da sojoji suka ce sun kutsa cikin dajin da maharan ke buya, ba tare da yin karin bayani kan aikin ceton ba.  A cikin 'yan shekarun da suka gabata dai, kungiyoyin masu aikata laifuka sun kashe fiye da fararen hula 2,600 a cikin 2021, lamarin da ya karu da  fiye da kashi 250% idan aka kwatanta da 2020, a cewar alkaluman kungiyar mai zaman kanta Acled.