Nahiyar Afirka na neman magance Ebola | Labarai | DW | 03.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nahiyar Afirka na neman magance Ebola

Ƙasashen Afirka 11 na shirin tinkarar cutar ta Ebola da ta kashe rayukan ɗarurruwan mutane a Gini da Liberiya da Saaliyo.

Ministocin kula da lafiya na ƙasashe 11 na Afirka sun amince da ɗaukan matakan gaggawa don shawo kan cutar Ebola da ke da saurin kashe mutun, a lokacin taron gaggawa da suke gudanarwa a birnin Accra na ƙasar Ghana. An dai fara taron ne a ranar Laraba na wannan makon, wanda a samu waklicin ƙasashen Senegal da Gambiya da sauransu.

Ƙididigar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar, ta nunar da cewar kusan mutane 470 suka rasu rayukansu daga cikin 760 da cutar ta kama su a ƙasashe uku da Ebola ta yaɗu a cikinsu, ciki kuwa har Gini Conakry da Liberiya da kuma Saliyo. Kawo yanzu dai babu wani magani ko kuma wani rigakafin wannan cutar ta Ebola da ke ci gaba tamkar wutar daji.

Mawallafa: Ramatou Issa Ouanke/MAB
Edita: Abdourahmane Hassane