Na'aurar nadar magana ta Germanwings
April 2, 2015Talla
Masu shigar da kara a birnin Marseille na kasar Faransa sun ce ma'aikatan ceto sun gano na'urar nadar magana ta biyu ta jirgin saman Germanwings da ya fadi a yankin tsaununkan kasar Faransa makon da ya gabata. Na'urar za ta ba da karin bayani game da tafiyar jirgin saman samfurin Airbus A320. Tun a ranar da jirgin ya fado aka gano na'urar nadar maganar ta farko, wadda bisa abubuwan da aka ji, mataimakin matukin jirgin saman ya rufe kaftin din a wajen dakin matuka, sannan da gangan ya yi setin jirgin ya fadi, ya halaka dukkan mutane 150 da ke cikinsa.