1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar ta kare sojojinta daga zargi

Abdul-raheem Hassan
August 29, 2018

Gwamnati ta kare jami'an sojinta da ke zargi da aikata laifukan yaki kan musulman Rohingya, bayan da Amirka suka bukaci a hukunta su kan sakamakon binciken Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/33yBz
Myanmar Aung San Suu Kyi
Hoto: Getty Images/AFP/Ye Aung Thu

Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da jerin shedun laifukan take hakkin bil'adama da ake zargin sojojin Myanmar da aikatawa cikin har da fyade da muzgunawa musulmai bayan barkewar rikici a jihar Rakhine. Gwamnatin Myanmar ta ce sakamakon binciken ba shi da tuhse balle makama, sabaoda babu jami'a MDD da aka ba wa damar shiga kasar domin gudanar da bincike.