Myanmar ta hana auren mata fiye da daya | Labarai | DW | 31.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar ta hana auren mata fiye da daya

Karkashin wannan doka dai duk wanda aka kama da mata fiye da daya wanda ba kasafai ake samu ba zai kwashe shekaru a gidan kaso.

Myanmar lässt 6966 Gefangene frei

Al'ummar Myanmar cikin yanayi na kunci

Mahukunta a kasar Myanmar sun kafa wata sabuwar doka da ta haramta wa al'ummar kasar auren mata fiye da daya kamar yadda rahotanni suka nunar a ranar Litinin din nan.

Wannan dokar ta hana auren mata fiye da daya ta zama cikon ta hudu cikin wasu dokoki da mahukuntan kasar ta Myanmar masu bin addinin Buda suka sanyawa hannu karkashin shugabancin Thein Sein, dokokin kuma da ake ganin an tsarasu ne da nufin gallazawa ga al'ummar Musulmi da ke a wannan kasa wadanda kuma suke zama marasa rinjaye.

Karkashin wannan doka dai duk wanda aka kama da mata fiye da daya wanda ba kasafai ake samu ba a wannan kasa, zai fiskanci hukunci na zama a gidan kaso tsawon shekaru bakwai.

Wannan kasa dai ta Myanmar ta shiga yanayi na fargabar tashin hankali tsakananin kabilu daban-daban tun bayan rikicin da aka gani mai nasaba da banbancin addini tsakanin mabiya addinin Buda da 'yan kabilar Rohingya da ke zama Musulmi a tsakiyar shekarar 2012.