1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Babban jami'in gwamnatin Aung San Suu Kyi ya mutu

Ramatu Garba Baba
March 9, 2021

Wani babban jami'i na hambararriyar gwamnatin Aung San Suu Kyi ya kasance mutum na biyu da ke mutuwa a hannun jami'an 'yan sanda a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3qPQt
Myanmar | Beerdigung von U Khin Maung in Yangon
Hoto: Str/REUTERS


Daya daga cikin manyan 'yan siyasar kasar Myanmar da aka kifar da gwamnatinsu ya mutu a hannun jami'an da ke tsare da shi. Zaw Myat Linn ya mutu ne a wannan Talata kamar yadda wani mukadashin hambararriyar gwamnatin jam'iyyar NLD ta Aung San Suu Kyi ya sheda.

Rahotanni na cewa, an kama Mista Linn daga birnin Yangon, lamarin da ba ya rasa nasaba da goyon bayansa ga zanga-zangar kin jinin sojin da suka kwace mulki da karfin tuwo. Kawo yanzu dai ba a fadi dalilan da suka yi sanadiyar mutuwarsa ba koda a ka tuntubi jami'an 'yan sandan da ya cika a hannunsu.


Myanmar ta fada cikin rikici bayan kwace mulki da sojoji suka yi a farkon watan Febrairu, inda daga bisani suka kama Shugabar gwamnatin da manyan mukarrabanta, sojojin sun ki amsa kiran shugabanin manyan kasashen duniya na mayar da mulki hannun Suu Kyi. Masu zanga-zanga kimanin sittin ne suka rasa rayukansu a yayin artabu da jami'an tsaro a yayin da wasu sama da dubu daya ke tsare.