A na zargin 'yan jarida da bayar da bayanan sirrin kasa
July 9, 2018Talla
An zargi 'yan jaridan da aikata wannan laifi ne a lokacin da suke tura rahotannin labarin rikicin kabilanci yankin Rakhine na al'ummar 'yan Rohingya. 'Yan jaridan da suka hada da Wa Lone, mai shekaru talatin da biyu da Kyaw Soe Oo, mai shekaru ashirin da takwas za su iya fuskantar hukuncin dauri na shekaru goma sha hudu muddun a ka tabbatar da laifin da a ke zarginsu a kai.
Mutanen biyu sun kwashi watannin bakwai a tsare a yayin da suke ci gaba da musanta laifin da a ke zarginsu da aikatawa.