1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muzambik na neman agajin duniya

April 30, 2019

Firamanistan kasar Mozambik Carlos Agostinho do Rosario ya ce batun sake gina kasar abu ne da zai dogara da taimako daga kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/3HgAf
Mosambik Zerstörung nach Zyklon Kenneth
Hoto: Reuters/OCHA/Saviano Abreu

A wata hirar da ya yi da tashar DW, firaministan ya ce bangaren abinci babu wata gagarumar matsala a yanzu, kayayyakin sake gina kasar ne babban kalubalen da ke a gabansu.

Kasar dai na fama ne da barnar da mahaukaciyar guguwa dauke da ruwan sama, da ta afka wa arewacinta a makon jiya.

Ofishin kula da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya ce guguwar mai karfin gaske ce ta aka taba gani a yankin kudancin Afirka.

Majalisar ta duniya ta kuma yi hasashen ci gaba da shatata ruwan na sama cikin kwanakin da ke tafe.

Akalla mutum 38 suka mutu a sabon ibtila'in, wasu sama da dubu 23 kuwa suka rasa muhalli.