1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da mutuwar George Floyd

Ines Pohl | Usman Shehu Usman SB
May 25, 2023

Mutuwar George Floyd shekaru uku da suka gabata ta zama abin tayar da hankali kan rikicin ‘yan sanda da nuna wariyar launin fata a Amirka. Masu laifin suna cikin kurkuku a yanzu.

https://p.dw.com/p/4RoDd
George Floyd Rembrance Event: 1 Year Anniversary
Hoto: imageSPACE/ZUMA/picture alliance

Minti tara da dakika 29 sun girgiza duniya shekaru uku da suka gabata. Bidiyon da wani mai wucewa ya ya dauka da wayar salula a Minneapolis ya bayyana rashin imani. Hakan ya nuna wani dan dan sanda farar fata Derek Chauvin ya danne gwiwarsa a wuyan George Floyd sama da mintuna tara yayin da yake rokon a bar shi ya numfasa yana kuma kiran mahaifiyarsa don neman taimako. Abokan aikin Chauvin Alexander Kueng, Tou Thao da Thomas Lane su kuma sun zuba ido. Robert Samuels marubuci wanda ya ce batun girman wariyarar launin fata akwai mamaki.

Karin Bayani: Rusa mutum-mutumin 'yan mulkin mallaka

Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata
Zanga-zangar adawa da wariyar launin fataHoto: Oliver Hurst/GES/picture alliance

An yi zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da cin zarafin 'yan sanda ba wai a cikin kasar Amirka kadai ba, amma har a kasashen duniya. A yawancin biranen Amirka, an sami dokar ta-baci a cikin kwanaki da makonni bayan 25 ga Mayu, 2020. Fushin shekaru da yawa na cin zarafi daga jami'an 'yan sanda farar fata, da takaici ga yawancin wariyar launin fata da aka yi la'akari da tsarin tsarin masu sa kaki ya rikide zuwa tarzoma, kona-kone da sauransu.

Daga karshe dai kotu ta yankewa dan sandan da ya kashe George Floyd daurin shekaru 40 a gidan yari, masanan cewa ba don duniya ta dau zafi kan bidiyon da aka yada ba, da ya fallasa kisan da 'yan sanda suka yi to kusan da babu wani hukunci mai karfi da 'yan sanda za su yi. Domin irin kisan da ganga mai alaka da wariyar launin fata ta sha faruwa a Amirka. Shugaba Joe Biden wanda ya hau mulki fadar White House shekara guda bayan aukuwar lamari, ya zo da manufar kawo sauyi kan ayyukan 'yan sanda, to amma  kungiyoyin kare hakkin mutane na cewa babu wani sauyi da aka samu a kasar Amirka a bangaren cin zarfin da yan sanda ke yi musamman ga bakaken fata.