Mutumin da zai gaji Mugabe ya koma kasar | Labarai | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutumin da zai gaji Mugabe ya koma kasar

Emmerson Mnangagwa wanda ake fatan rantsarwa a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabuwe ya isa kasar daga Afrika ta Kudu inda ya baiyana a karon farko tun bayan da ya bar kasar.

Simbabwe Emmerson Mnangagwa (Getty Images/M.Longari)

Emmerson Mnangagwa na jinjina ga magoya baya a Zimbabuwe

A jawabinsa, ya yabawa sojin kasar bisa jajircewa da kuma namijin kokarin da suka yi wajen karbe iko cikin ruwan sanyi, ya ci gaba da cewa kasar na bukatar sauyi na inganta tattallin arziki da samar da zaman lafiya da ayyukan yi ga kowa da kowa, daga karshe ya ce Zimbabuwe na bukatar hadin kan kasashen duniya don tabbatar da kafuwar wannan sabuwar demokradiyar da ta samu. A ranar Juma'a mai zuwa ake sa ran rantsar da shugaban da zai kasance na riko kafin a gudanar da zabe a shekarar 2018

Ana ganin korar Mnangagwa da Robert Mugabe ya yi shine sanadiyar hambarar da shi da sojoji suka yi a makon da ya gabata. Mugabe ya amince da yin murabus ne bayan ja-in-ja da sojoji da suka yi masa daurin talala. Ya yi shekaru 37 yana mulkin kasar Zimbabuwe.