1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin kunar bakin wake a Pakistan

Ramatu Garba Baba
January 30, 2023

Mutum akalla 59 yanzu haka aka tabbatar sun mutu a sakamakon wani kazamin harin kunar bakin wake da wani ya kai kan masu ibada a kasar Pakistan.

https://p.dw.com/p/4Ms5n
Pakistan | Explosion in einer Moschee in Peshawar
Hoto: MAAZ ALI/AFP/Getty Images

Rundunar 'yan sandan kasar Pakistan ta ce, mutum kimanin 59 ne suka mutu a sakamakon wani kazamin hari da ta kira na ta'addanci, sanarwar rundunar ta kara da cewa, maharin ya tayar da abin fashewa ne a cikin wani masallaci da ke daf da harabar ginin ofishin 'yan sanda a kusa da birnin nan na Peshawar, akasarin ginin masallacin ya rushe tare da danne masu ibada. 

Akwai fargabar a samu karuwar asarar rayuka ta la'akari da munin harin da ya raunata wasu fiye da dari. Akasarin wadanda suka mutun jami'an 'yan sanda ne, kawo yanzu babu kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai harin a kasar da ta jima tana fama da hare-hare masu nasaba da ta'addanci.