Mutum na takwas ya kamu da Ebola a Mali | Labarai | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum na takwas ya kamu da Ebola a Mali

Gwamnatin ta Mali ta ce ta killace mutumin sannan kuma ta ce tana sa ido a kan wasu mutane 271 waɗanda suka yi mu'ammula da mutumin.

Hukumomin kiwon lafiya a ƙasar Mali sun ba da sanarwar cewar an samu mutum na takwas da ya kamu da cutar Ebola a ƙasar. Tun da farko a ranar Asabar da ta gabata ofishin ministan kiwon lafiya na ƙasar ya sanar da cewar an samu ƙarin wani mutumin da ya kamu da cutar.

Gwamnatin ƙasar ta Mali ta ce an killace mutanen a wata cibiya ,ana jinyarsu sannan kuma ta ce ana sa ido a kan wasu mutane 271 da suka yi cuɗanya da waɗanda ake jinyar.