1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutanen da ke cikin jirgin da ya bata a teku sun mutu

June 23, 2023

Bayanai daga Amurka sun tabbatar da cewa babu wani daga cikin mutanen da ke jirgin da ake nema cikin kwanakin nan a tekun Atlantika da ya rage da sauran numfashi.

https://p.dw.com/p/4Sy9V
Hoto: Scott Eisen/Getty Images

Dakarun da ke gadin gabar tekun Amurka, sun ce dukkanin fasinjoji biyar da ke cikin jirgin ruwa mai nutsewa wanda ya bata a karkashin teku sun mutu.

Da safiyar ranar Alhamis ne dai jami'an tsaron gabar tekun na Amurka suka ce an gano wani wajei da ke cike da tarkacen jirgin da suke ciki a kusa da jirgin nan na Titanic wanda ya nitse yau shekaru 111.

A ranar Lahadin da ta gabata ne jirgin wanda na kamfani mai kula da zirga-zirgarsa ne wato Titan, ya bata dauke da mutanen su biyar.

Kamfanin ya ce mutanen biyar masu tafiye-tafiye ne irin na bincike na hakika da suka hadu a kan manufar ganin kwakwaf a karkashin ruwa.